'Za Mu Hadu a Kotu,' Jigon APC Ya Yi Barazana Kan Nadin Abdullahi Ganduje

May 2024 · 2 minute read

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Tsohon darakta janar na kungiyar gwamnonin jihohin APC na PGF, Salihu Lukman ya yi barazanar maka jam’iyyar APC gaban kotu bisa karya kundin tsarin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

"Da wahala", Jigon APC ya gaji da kame kamen Tinubu wajen gyara Najeriya kamar Lagos

Salihu Lukman wanda kusa ne a APC ta cikin wata budaddiyar wasika da ya aikewa da shugaban kasa Bola Tinubu ya ce uwar jam’iyyar ta saba sashe na 221 zuwa 229 a kundin tsarin mulki.

tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na Arewa ya ba gwamnatin Bola Ahmed Tinubu wa'adin 7 ga watan Yuni 2024 domin gyara kura-kuran da aka tafka, kamar yadda The Guardian ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Nadin Ganduje kuskure ne,' Salihu Lukman

Jigo a jam'iyyar APC Salihu Lukman ya bayyana nadin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kin gudanar da babban taron jam'iyya a matsayin sabawa doka.

Ya ce nada Ganduje ya saba da dokar karba-karba da jam'iyyar ta amince da shi. Wasu jiga-jigai a jam'iyyar na dauke da wannan ra'ayi kamar yadda Leadership News ta tattaro.

Kara karanta wannan

'Ba 'yan Jam'iyya ba ne,' matasan APC sun yi martani ga masu son tsige Abdullahi Ganduje

Salihu Lukman ya kara da cewa ya nemi ganin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin su gana kan matsalolin jam'iyyar amma hakan ya ci tura.

An rusa masarautun da Ganduje ya kafa

Mun kawo muku labarin cewa majalisar dokokin jihar Kano a yau Alhamis ta rushe dukkanin masarautun da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta nada.

Majalisar ta kuma rage darajar maarautun Gaya, Karaye da Rano matsayi na biy. Sannan ta bawa gwamna Abba Kabir Yusuf damar kiran masu nada sarki a nada sabon sarkin Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ6f5ZxbGaykWK6tnnHmpuuZZFiuLDA1Gahop%2Bfo3qivMJmsJplqZ56o63RmrGappFiuKK6jKeYnaGeYq6jsNSlo5qgmWK0orrDrqGeZw%3D%3D